Daga Datti Assalafiy
Wadannan kungiyoyin sharri mallakin turawa makiya Allah da addininSa abinda Allah Ya fada mana a kansu shine ba zasu ta6a yarda damu ba har abada face sai munbi hanyarsu mun zama su.
Abinda wadannan kungiyoyin sharri suka fake dashi shine wai su zasu tallafawa bil’adama ne ko da ‘dan ta’adda ne, to wannan barnace, makirci ne da makarkashiya da sabon salo na mulkin mallaka.
Wadannan kungiyoyin sharri da suka mamaye jihar Borno an dade da gane mugun nufinsu, suna hada hannu da wasu manyan maciya amanar Nigeria masu fada aji, abinda zai tabbatar muku da wannan shine kasa da wanni 10 da babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole ya dakatar da ayyukan kungiyar UNICEF saboda taimakon ‘yan ta’adda da kungiyar take sai aka zafafa kira ga kwamandan rundinar wanda ala tilas ya janye dakatarwan da yayi musu.
A yanzu haka jama’a idan dare yayi kamar karfe daya zuwa biyu na dare sai kaji jirgin wadannan kungiyoyin sharri yana kai-kawo a dazukan Borno, sannan kuma taimakon abinci da sukeyi a baya sun janye a halin yanzu, ma’aikatan da suka dauka a farko yanzu sun zubar dasu duk arna wadanda ba musulmi ba suke dauka aiki, wadansu arnan daga Jos aka daukosu, sauran kuma mutanen kudu ne inyamurai, yarinya ‘yar karama shekaranta 15 ana biyanta naira dubu dari biyu da hamsin zuwa dari uku.
Mazan ‘yan asalin jihar Borno an sallamesu a aiki, idan kuma kai mai fada aji ne zasu karbi hayan gidanka akan naira miliyan talatin har zuwa miliyan dari biyu, sannan a cikin ma’aikata ‘yan mata da suka taba yin aiki dasu yanzu ko batun auransu mutane basayi, saboda kusan gaba dayansu suna da cuta mai karya garkuwan jiki da suka samu lokacin da suke aiki da kungiyoyin sharrin, sannan kuma sun raba aure bila adadin.
Wallahi jama’a ko yau rundinar sojin Nigeria ta fatattaki wadannan kungiyoyin sharri aka koresu daga jihar Borno sun gama damu, saboda kungiyoyin sharrin suna haduwa da ‘yan Boko Haram a duk lokacin da suke son haduwa, sannan kuma suna taimaka musu da kayan abinci, magunguna da kayan masarufi har ma da kudi.
Garin Abadam na jihar Borno tana kan iyaka da Nijer, kogi ne kawai ya raba Abadam da Nijer, yanzu haka jama’a akwai kimanin ‘yan Boko Haram sama da dubu biyu wadanda kungiyoyin sharri suka hada hannu da Gwamnatin Nijer aka sakesu, sai aka basu wani takarda idan ka kuskura kace musu ‘yan Boko Haram wallahi sai kayi shekara biyu a gidan yari, sannan kuma yanzu sune suka zamo wani sabon fiitina.
Lokacin da wadanna ‘yan ta’addan sama da dubu biyu kungiyon NGOs suka wuce musu gaba gwamnatin ‘kasar Nijer ta musu afuwa sai sukaje suka bunne manyan Makamansu a karkashin ‘kasa, sai suka mika kansu da wasu makamai kalilan, sai aka wankesu sukazo suka zauna da sauran mutane wadanda su ba Boko Haram bane.
Wadannan kungiyoyin sharri (NGOs) suka baiwa ‘yan Boko Haram din da suka mika makamansu ga gwamnatin Nijer abubuwa kala-kala da sauran tallafi, daga bisani su wadannan ‘yan ta’adda da suka mika makamansu sun sake haduwa suka tafi suka tona makamansu, suka kwace motocin yaki na sojojin Nijer sama da hamsin a kan iyaka, sukayi gaba abinsu zuwa gurin Albarnawiy na ISWAP dake da sansani a yankin tabkin chadi, yanzu haka man fetur da komai na abinda suke bukata suna samunshi ta bodar Abadam da ke iya da ‘kasar Nijer.
Suwaye sukayi sanadin haifar da wannan sabon fitina? amsar itace kungiyoyin sharri.
Tsakanin sojojin Nigeria da wadannan kungiyoyin bada agaji suwaye suka tallafawa ‘yan ta’adda? amsa kungiyoyin sharri.
Tsakanin kungiyoyin sharri da sojojin Nigeria suwaye sukafi lalata ‘yan mata a dalilin wannan yakin? amsa itace kungiyoyin sharri, watanni baya mun saka muku labarin wani babban likita a Maiduguri wanda yace yana da record na ‘yan matan da suke aiki da kungiyoyin sharrin wadanda aka dirka musu cikin shege sama da dari, kuma da yawa daga cikin ‘yan matan da aka yiwa cikin shege an saka musu cutar kanjamau.
Mai yasa kungiyoyin sharri basa fitar da irin wannan rahoto na 6arna da cin zarafin ‘ya’yan mutane da sukeyi? sai dai kawai saboda makarkashiya su hada rahoto na karya su fitar akan sojojin Nigeria wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen tabbatar da tsaron Nigeria.
Yaa Allah Ka mana maganin wadannan kungiyoyin sharri da suke cutar damu.
Post a Comment