(a cikin littafinta mai suna Jima'i Domin Ma'aurata)
Kamar mata, suma maza sunada nasu abubuwan da yakamata su aiwatar kamin lokacin gudanar da jima'i da matayensu, haka kuma sanin wadannan abubuwa tare kuma da aiyawatar dasu ga duk wani magidanci namiji ya zamemasa wajibi ganin irin wadannan shirye-shirye ne maigida zai samu damar gamasar da matarsa tare kuma da samar da yanayi na jima'i mai dadi a junansu .
Duk da yake abubuwan da ake bukatan maza su aiwatar kamin jima'i da matayensu suna kamaceceniya da abubuwan da ake bukatar mata suma suyiwa mazajensu kamin jima'i, gyaran dakin jima'i ne kadai aka cireshi daga cikin jeren abubuwan dake cikin shirye shiryen mata da babu a cikin na maza. Haka nan kuma ana bukatar kamar yadda matansu zasuyi amfani da wadannan abubuwan sau da kafa, haka suma ake umurtarsu dasu yi amfani dasu domin samarwa juna kwanciya ta aure mai annashuwa.

1,Abinci da Namiji zai ci kamin jima'i: Kamar yadda mata suke da abincin daya kamata su ci ko su sha kamin tinkarar Mazansu da jima'i, haka suma mazan sunada nasu abinci ko abinsha daya kamacesu da ci ko su sha kamar dai su matan. Haka zalika kuma da akwai abinci ko abinshan da aka haramtawa maza amfani dasu a kullum ko kuma kamin yin jima'i.
Shi namiji ba kamar mace bane a wajen cin abincin jima'i, domin a kullum ana bukatar namiji ya ci abin ya koshi kamin ya tinkari matarsa da jima'i, duk da yake ana bada shawaran kada magidanta su cika cikinsu fal har wuya da koshi kamin jima'i, amma amfi bukatar namiji ya koshi mintuna 30 kamin lokacin ganin yaddda gudanar da jima'i yake bukatar karfi da kuzari shi yasa ake bukatar maza su zama babu alamun yinwa a tare dasu komin kankantarsa.
Babu damuwa da irin abincin da namiji zai ci mai nauyi ko mara nauyi, abun bukata kawai shine daya tabbatar da cewa ya koshi.
Abinci irinsu danyen rogo baya ga dukkan wani nau'i na abinci mara cutarwa ga mutum tuwo ko shinkafa ko taliya Shan zuma, danyen madara rake abubuwa ne da suke da amfani sosai a jikin maza musamman idan suka samesu kamin jima'i a cewar likitoci na jima'i.
Haka kuma duk wani abu mai zaki, tsami yaji namiji ya kauracewa cinsu daf da lokacinda zaiyi jima'i saboda illar da suke yiwa maza musamman ga masu yawan ci ko shan su. Sai dai jan kanwa da lemun tsami wani sirri ne na kara karfin gaban maza tsabanin yadda wasu suka yi masu mummunar fahimta. Sai dai kuma duk namijin dayayi amfani awa guda kamin jima'i, suna iya zama illa a wajensa. Akalla ana bukatar namiji ya samu awannin 6 zuwa bakwai kamin yayi jima'i bayan yayi amfani da lemun tsami ko kuma jan kanwa, domin kamin wannan lokacin ya fitsarar da duk wani dattin dake mararsa ko kuma yayi zawayin dattin dake cikinsa kana ya samu kasalar jiki na dan wani lokacin na awanni daga bisani kuma sai ya soma jin dai-dai.


2,Wanka Kamin Jima'i": Suma maza ya zamemasu dole su tsaftace jikinsu kamin suyi kwanciyar jima'i da matayensu, kamar yadda kowani namiji yake bukatar ji kuma da ganin matarsa ko ina a jikinta tsaf, haka ita matarsa take bukatar ganisa, don haka muddin namiji yana bukatar matarsa ta sakarmasa jiki sosai a lokacin da suke gudanar da jima'i dole ne ya tsaftace ko ina na jikinsa.
Kamar yadda mata suke da wuraren da zasu yi la'akari dasu a lokutansu na wankan jima'i, haka suma maza da akwai wasu wuraren da dolene sai sun wankesu yake tabbatar da cewa sunyi wankan jima'i domin gudn takurawa matayensu da warin jiki ko kuma tsamin jiki ko wani irin.

Tabbatar da tsaftace baki shine abu na farko da duk wani magidancin daya shiga wankan jima'i zai fara dashi, ya tabbatar da cewa babu wani abu na wari ko yami dama karni daya rage a bakinsa, kuma ya tabbatar da cewa ba zai sake saka wani abunda zai sanya wari a bakinsa ba bayan ya fito daga wankan. Dole ne namijin daya shiga wankan jima'i ya kasance ya tsaftace hamatansa, matsaimatsinsa, duburansa, tsaftace gashin gabansa idan mai barin gashi ne tare kuma da wanke gabansa sosai musamman 'ya'yan marainansa.
Wadannan sune abubuwa masu mahimammncin a kula da su ga dukkannin namijin daya shiga wankan jima'i a jerin abubuwan da maza ya kamata su farayi kamin kwanciyar jima'i. Suma maza dole ne suyi amfani da sabulu mai kamshin da bai cutarwa ga matayensu kamar yadda aka shawarci mata suma suyi amfani da sabulu a lokutan wankasu mara cutarwa ga mazajensu.

3,Kwalliya Kamin Jima'i: Shima kwalliyar namiji kaimin jima'i tamkar kwalliyar macece kamin jima'i, dole ne ya kasance ya shafa mai mai kamshi da kuma turare mai kamshin dake burge matarsa a lokacinda yazo kwalliyarsa ta jima'i.
Wasu mazan na gani bai zama dole ba su yiwa matansu kwalliya kamin su kwanta jima'i, karamin tunaninsu da fahimtarsu matane kadai ya zamewa dole, wannan batun ba haka yake ba, domin watan macen kwalliyar da namiji zai yine a wannan lokacin yake iya motsa mata sha'awarta, don haka ba tsari bane da zaran namiji ya fito daga wankan jima'i kawai ya goge jikinsa da tsumman goge jiki ba tare da ya lailaye jikinsa da kayan kamshi ba ya nemi kwanciya da matarsa, hakan maimakon ya karawa mace sha'awar jima'i saima ya rage mata sha'awar.

4,Ado Kamin Jima;i- Suma maza dole su rika burge matansu a lokacin da sukayi adonsu na jima'i tamkar yadda matayensu suke burgesu. Kada maigida ya kammala kwalliyarsa da kyau wajen adonsa na jima'i kuma ya bata tsarin abubuwan daya yi baya. Domin wasu mazan a lokutansu na adon kwanciyar jima'i basu yi adon da zai tayar da hankalin mace.
Ba tsari bane namiji yayi saurin fito da tsiraicinsa ga mace tunma gabannin wasannin motsa jiki. Yana da kyau da zaran namiji yazo adon jima'i ya samu kaya shima mai shara-shara ya sanya, ya kuma tabbatar da cewa kayan dake jikinsa.

Akasarin maza basuda masaniyar cewa, mata da yawa suna jika wandunasu da ruwan sha'awa a lokutan da suka ga mazajensu cikin kananan gajerun wandunan nan da akafi sani da suna Boxers. Mata da aka zanta dasu sun nuna cewa da zaran sunga mazajensu a lokacin kwalliyarsu na jima'i sun saka irin wadannan gajerun wandunan nan take suke fara jin sha'awa ta kamasu. Haka kuma mata na sha'awar ganin mazajnesu a lokacin kwalliyarsu na jima'i sun saka singiiletin da zai fito da girjinsu kuma ya bayyana gashin kirjinsu idan masu gashi ne a jiki. Wasu kuma matan sukace babu abunda ke daga masu hankali na sha'awa irin ganin mazansu sun sanya doguwar riga amma kuma babu wando a jiknsu.

5,Yanayin Lokacin Jima'i: Ba maza bane kadai suke bukatar yanayi da lokaci mai kyau ba a shirye shiryensu na jima'i, suma mata suna bukatar mazajensu su basu lokacin da suka tabbatar da cewa babu wani abunda zai gifta a wannan tsakanin har sai bayan sun biyawa juna bukatarsu ta jima'i. Dole ne kowani namiji ya tabbatar da cewa ya kammala duk wasu hidimomin gabansa abunda ya rage kawai a wannan lokacin shine na jima'i da matarsa kamin ya soma wannan shirye shiryen na kwanciyar jima'i. Dole ne a kashe waya ko kuma a sanyashi a tsarin shuru kamin soma jima'i domin gudun kada wata waya ta shigo da mugun labarin da zata katsai sha'anin.

A wannan babin ma'aurata a yanzu sun fahimci cewa jima'i yana bukatar shiri na musamman kamin ma'aurata su tinkareshi, ba haka nan kawai bane magidanta zasu afkawa kawunansu da ci ba, dole ne idan har suna bukatar jima'in da zasu gamsar da junansu, sai sun samar da lokacin da zasu gudanar da wadannan shirye shiryen koda kuwa a kullum na duniya sai sunyi jima'i. Da fatan ma'aurata sun fahimci abunda wannan babin yake karantarwa.

Source from: HAUSALOADED.COM

Post a Comment

 
Top