Daga Datti Assalafiy

Rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwa ta hannun kakakinta Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka tace kungiyoyin kare hakkin bil’adama na duniya (a Nigeria) suna aiki tukuru domin ganin sun tarwatsa gwamnatin Nigeria.

Rundinar sojin tace kungiyoyin kare hakkin bil’adaman da suke da reshensu a Nigeria sun kauce daga hakikanin tsarin manufar kafasu da akayi a ‘kasar Birtaniya domin su tallafawa al’umma, akwai bayanan sirri da ya tabbatar da cewa za’ayi amfani da kungiyoyin domin a tarwatsa gwamnatin Nigeria, a cewar rundinar sojin.

An fahimci wannan mummunan ajanda na kungiyoyin kare hakkin bil’adama a Nigeria ta dalilin yin 6atanci da sukeyi ga hukumomin tsaron Nigeria, tare da daukar nauyin kungiyoyin sharri domin suyi zanga zangar nuna kin jinin hukumomin tsaron Nigeria, da kuma fitar da kalaman 6atanci akan shugabancin rundinar sojin Nigeria, sannan wadannan kungiyoyi sharri sun dauki shekara da shekaru suna daukar nauyin kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram, kungiyar shi’ah magoya bayan Zakzaky, yanzu kuma suna amfani da rikicin fulani makiyaya da manoma domin su cimma mummunan kudurinsu na tarwatsa gwamnatin Nigeria.

A yanzu haka wadannan kungiyoyin sharri wadanda ba na gwamnati ba (NGOs) suna dab da fitar da rahoton karya akan rundinar sojin Nigeria, don haka ‘yan Nigeria kar su damu da batancin wadannan kungiyoyin hare hakkin bil’adama a Nigeria domin babban burinsu shine su tarwatsa gwamnatin Nigeria da wargaza al’ummarta.

A yanzu haka rundinar sojin Nigeria bata da wani za6i fiye da ta dauki matakin yin kira a kulle dukkan ofishin wadannan kungiyoyin kare hakkin bil’adama na duniya a Nigeria matukar suka cigaba da shirya makarkashiya ga tabbatar da tsaron Nigeria.

Rundinar sojin Nigeria tana rokon jama’a su yada wannan sanarwan zuwa ga duk inda ya dace. Sanarwa daga Kakakin rundinar sojin Nigeria Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka.

Babban manufar fitar da rohoton karya da kungiyoyin kare hakkin bil’adaman sukeyi akan hukumomin tsaron Nigeria musamman rundinar soji shine domin a hana gwamnatin Nigeria sayen makaman yaki na zamani wanda za’ayi amfani dashi a yaki ‘yan ta’adda, to su kuma kungiyoyin sharrin ba burinsu a kawo karshen ta’addancin ba a Nigeria saboda ta hakane suke samun makudan kudade, don haka zasu cigaba da yin amfani da rahoton karya domin tabbatar da cewa hukumomin tsaron Nigeria basu samun damar sayen makaman yaki na zamani ba.

Idan za’a tuna watannin baya kadan Ministan Tsaron Nigeria Malam Mansur Dan Ali ya fitar da rahoto akan wadannan kungiyoyin sharri wadanda suka mamaye jihar Borno ya tabbatar da cewa kungiyoyin suna tallafawa ayyukan ta’addancin Boko Haram saboda basaso a kawo karshen ta’addancin, domin ta sanadin ta’addancin ne suke samun makudan kudadensu.

Ku tuna da bayanin da nayi shekaran da ta gabata (2017) akan ayyukan sirri (secrete operations) na wadannan kungiyoyin sharri, tsakani da Allah babu wani mataki da ya ragewa gwamnatin Nigeria fiye da ta kori wadannan kungiyoyin sharri tunda yanzu an gano makircinsu a hukumance.

‘Yan Nigeria muyi kokarin dagewa da addu’ah Allah Ya wargaza aniyar wadanda suke yiwa tsaron Nigeria makarkashiya.

Post a Comment

 
Top