Daga Maje El-Hajeej Hotoro

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata 11 a Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge bisa zargin shirya shagalin auren madigo, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito.

Jami’in sintiri na Hukumar Hisbah Nasiru Ibrahim ya bayyana cewa, sun samu bayanan sirri na cewa, Safiyya Yobe ce za ta auri Fatima Gezawa yayin shagalin. Wanda hakan ya sa suka kai sumame gami da cafke Mata 11 ciki har da ANGUWA (Wacce zata yi auren) da AMARYA (Wacce za a aura).

Sai dai daya daga cikin matan da aka kama Fati Jaririyar Zuciya ta bayyana cewa, sun shirya wannan shagali ne domin taya AMARYA Fatima Gezawa ba ta mukamin mataimakiyar shugabar gidan rawa, wanda ANGUWA Safiyya Yobe ce shugaba.

A Afirilun 2007, an samu makamancin wannan sumame a jihar Kano inda aka zargi wata ‘Aunty Maiduguri’ da laifin AUREN MATA hudu (4) yayin shirya shagalin tarawa wata Kilaki kudi da za ta auri Namiji.

Post a Comment

 
Top