Daga Datti Assalafiy

Shekaran jiya Saman Na Buhari yake bada labarin cewa ina zaune cikin daren nan wajen teburin mai shayi anan cikin garin maiduguri ana musun siyasa akan Buhari da Atiku, sai wani daga gefe yace duk mai zagin Buhari anan bashi da hankali, sai ya dauko labari yace dasu kun manta abinda yafaru da Alhaji Modu Bor da matar shi a 2014?

labarin shine kamar haka:

Alhaji Modu bor mazaunin garin Maiduguri ne a anguwar Budum, shidai wannan bawan Allah Alhaji Madu Bor matansa 2 suna zaune gida, daya amaryar tana da ciki, wataran bayan magariba sai nakuda yakama amaryar, gashi gari akwai dikar ta baci (curfew) bafita ba shiga balle ace akai asibiti, matar sai faman nakuda take duk hankalin ‘yan gidan ya tashi har uwar gidan Alhaji Modu Bor, sabida yaro sai yazo kamar zai fita sai yaki, matar kuka take tana zan mutu fa, haka uwar gida itama tana kuka tana rarrashinta duk da kishiryarta ce amman ta tausaya mata.

Kawai uwar gida tace da maigidan nasu kaje kasami wadannan sojojin dake kusa da gidanmu ka tsaya daga nesa ka daga hannayenka sama kayi musu bayani, haka Alhaji Modu ya dauki shawaran uwar gida yaje ya tsaya daga nesa ya daga hannayensa sama yayi wa sojoji bayani irin hali da yake ciki kan su taimaka masa su dauki matarshi a motansu suka ta asibiti, amman sojojin sunki sauraransa saboda ansha yaudaransu haka ana kawo musu hari, sukayi masa barazana yafice daga wajen ko su harbeshi, haka bawan Allah yana kuka ya koma gida.

zuwansa gida ya samu uwar gida kuka amarya mai nakuda kuka, shima Alhaji Modu kuka, suna cikin wannan halin da misalin karfe daya na dare sai amarya tace da uwar gida nasan ni bazan kai gobe ba ki yafe min duk wasu laifuka da nayi miki, kuma kici gaba da yi min addu’a samun rahamar Ubangiji, nan uwargida ta yafe mata, amarya tace da uwar gida a kawo mata ruwa tasha, uwargida ta fita kawo ruwa sai tace da mijinta ga yayata kariketa amana, ni zan tafi inbarku tare, daman tare na sameku Allah yahada kanku.

Zuwan uwargida da wuya sai amarya takama salati tana maimaitawa can sai tace ga garinku, nan uwar gida da ta tabbatar amarya ta bar duniya itama ta yanke jiki ta fadi a sume, tashin hankali kan tashin hankali ma Alh Modu, uwargida itace bata farfado ba sai can wani lokoci ta tashi tana kuka, washe gari aka dauki amarya aka kaita makoncinta, bayan shekara da faruwar wannan abun uwargida ta haihu aka samu ‘ya mace aka sa mata suna Fatima wato sunan amaryar kenan.

Shine mai labarin yaci gaba da cewa yanzu a garin Maiduguri ko karfe nawa idan marar lafiya ne matukar kana da mota to zaka iya kai marar lafiyanka asibiti.

Allah Mungode maka da zaman lafiya da Ka bamu
Allah kada Ka sake maimaita mana irin wannan rayuwar masifa da bala’i.

Post a Comment

 
Top