Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, ya ce Allah ya yi magana da shi dangane da lokacin da zai mutu.
Gwamnan wanda a kwanannan ne ya cika shekaru 69, ya ce Allah ya bayyana mishi cewa zai mutu a shekaru 27 masu zuwa, a lokacin ya cika shekara 96 a duniya.
Ajimobi wanda suriki ne ga gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayi shagalin zagayowan daren bikin Kirsimeti da aka gudanar a birnin Ibadan sannan da kuma tayashi murnanr cika shekara 69. Kamar yanda majiyarmu ta Daily Post ta ruwaito.
Ya ce “Allah ya yi magana da ni dangane da Lokacin da zan Mutu. Ya fada min lokacin da zan mutu.
“Allah ya ce min zan mutu a shekara 27 nan gaba. Ya ce zan mutu ina da shekara 96. Kar ku min kuka, Allah ya mini tanadi mai kyau”. Inji Gwamna Ajimobi.
Daga karshe gwamnan ya bukaci ‘yan jihar da ma Najeriya da su yi amfani da lokacin Kirsimeti domin su yi adu’ar sake samun nasarar jam’iyar APC da dan takaran gwamnan jihar, Bayo Adelabu a zaben 2019.
Post a Comment