Tsafi: Mun Haƙura Da Sanya Dan Kanfai – Inji ‘Yan Matan Jami’a

Kafatanin ‘yan matan manyan makaratun jihar Delta da ke a kudancin Nijeriya sun bayyana yanke hukuncinsu na hakura da sanya dan kanfai sakamakon matsafa da suka addabe su da satar wandunan nasu suna aikata tsafin neman kudi da su.

Wannan lamari ya yi kamari da har ya kai wadannan matsafa da a can Delta din suke kira da Yahoo nBoys suna fashin dan kamfai daga jikin budurwa ta hanyar nuna mata bindiga, ita kuma dole ta cire ta basu don tsira da rai.

Wanduna mata masu shekaru tsakanin 14 zuwa 35 a jihar ta Delta ya zama tamkar ruwa a sahara, lamarin da ya sanya har sai da gwamnatin jihar ta fito haikan wajen yaki da barayin dan kamfan.

Jaridar Punch ta rawaito cewa farashin dan kamfai da budurwa ta yi amfani da shi musamman wanda akwai jinin al’ada a jiki na kaiwa har Naira dubu dari uku da hamsim (N350,000) a garin Asaba.

Jaridar ta Punch ta rawaito cewa, ‘yan matan jami’ar jihar ta Delta da ke da matsuguni a garin na Asaba sun bayyana cewa hanya daya da suka dauka na tseratar da kansu daga wadannan matsafa shi ne na daina sanya dan kamfai gaba daya.

Wata dalibar jami’ar ta jihar Delta ta shaidawa jaridar cewa: “Mun samu labarin cewa wadannan matsafa na yin amfani da dan kamfan mata ne wajen yin tsafin kudi, kuma da zarar sun yi tsafi da wandon, to fa sai mai wandon ta fara zubar jini ba ji ba gani. Wani lokaci ma an ce har da aman jini har sai ta mutu. Tun lokacin da muka samu labarin cewa har fashi da makamin dan kamfan ake yi a jikin mace, kawayena uku sun daina sanya dan kamfai da tsira da ransu da lafiyarsu.”

An ce ko a makon da ya gabata a sai da wasu maza biyu suka tare wata daliba suka kwace dan kamfan da ke jikinta ta karfin tsiya. Wannan ya faru ne a kan titin Titin Anwai a nan cikin garin Asaba da misalin karfe 8:00 na dare. Tun lokacin da wannan lamarin ya faru, ba a sake ganin yarinyar ba har yau har gobe.”

Ita ma wata dalibar kwalejin ilimi da ke a garin Asaba mai shekaru 22 da h

Post a Comment

 
Top