Boko Haram Sun Kwace Garuruwa Hudu A Jihar Borno Bayan Sun Fatattaki Sojoji

…sun daure hannayen wasu sojoji sun yi gaba da su

Da yammacin jiya Litinin da misali karfe 05:00pm, mayakan Boko Haram suka afkawa garuruwan KUKAWA, GUDUMBALI, CROSS KAUWA da BUNARI. Kuma dukkanin sojoji dake yankin an fatattake su, kamar yadda wata majiya daga daya daga cikin yankunan ta shaidawa RARIYA.

Majiyar ta kara da cewa bayan kwace garuruwan, ‘yan Boko Haram din sun daure hannayen wasu sojoji da ba a san adadin su ba, inda suka yi awon gaba da su har kuma zuwa yanzu ba a samu labarin su ba.

A halin yanzu garin BAGA kadai ya saura a hannun gwamnati. Shi kuma babu hanyan shiga da fita a yau din nan saboda an kwace Cross Kauwa daga hannun soja.

Post a Comment

 
Top