Shahararren malamin addinin Islaman nan, Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya kalubalanci gwamnatin tarayya kan ta sakan wa masu mas’uliyya kan makarantun Tsangaya zarafi da cikakken damar gudanar da makarantun domin samun nasarar inganta karatun Amajiranci a fadin kasar nan. Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kiran ne a lokacin da ke jawabi a sa’ilin yayen daliban dubu daya da dari shida da saba’in da takwas 1,678 da suka samu Haddace Alkur’ani a karkashin cibiyarsa da ke fadin kasar nan, taron wanda ya gudana a Abubakar Tafawa Balewa Stadium da ke Bauchi, ya ce masu mallakin makarantun Tsangaye suke da alhakin da cikakken damar inganta karatun Amajiranci a fadin kasar nan, ya shaida cewar muddin ana son inganta tsarin Amajirancin dole ne a sakan wa masu Tsangaya mara kan shirin. Sheikh Dahiru wanda ya samu wakilcin babban dansa, Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya ci gaba da cewa, “tare da hadin guiwar Tsangaya za a samu nasarar inganta tsarin karatu a Arewacin Nijeriya, wanda hakan zai iya rage yawaitar masu gararanba a kan titina,” Inji Shehi Ya bayyana muhimmancin haddar Alkur’ani, kana ya bukaci musulmai da masu ruwa da tsaki da su sanya hanu waje guda domin kyautata ilimin Kur’ani da ilimin addinin Islama don janyo wa Nijeriya ci gaba ta fuskoki daban-daban.


 Dahiru Bauchi ya taya daliban da suka samu nasarar Haddace Alkur’anin, kana ya kuma taya iyayensu murna da kuma kiransu da suke kara kula da ‘ya’yan nasu domin ci gaban addinin Musulunci. Darakta a fannin ilimi na cibiyar ‘Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation’, Sayyadi Aliyu Sise Sheikh Dahiru ya yi karin haske kan daliban da suka samu nasarar Haddar a wannan shekarar a fadin kasar nan, ya ce yara 380 ne suka samu nasarar haddar a jihar Bauchi, Kano mai dalibai 268, Gombe kuma yara 63 , sai Kaduna mai dalibai 63, Adamawa 15 , Kwara 38 da kuma jihar Kaduna mai adadi mafi tsoka da suka samu nasarar haddace Alkur’ani a wannan shekarar a karkashin cibiyar Dahiru Bauchi, inda jihar Katsinar ta tashi da adadin yara 571. Ya kuma kara da cewa yara 230 daga makarantun Islamiyyoyi daban-daban ne suka samu nasarar karantar Kur’ani izi 60 ba haddaba (tartili). Shugaban daya daga cikin makarantu mallakin Shaikh Dahiru Bauchi mai suna Madrasatu Markazussakafiyyil Islam da ke Kobi a cikin garn Bauchi, Mallam Hassan Adam Dahir Markazi ya bukaci iyaye da suke baiwa ‘ya’yansu dukkanin goyon baya da tallafin da ta dace domin samun nasarar daukar dukkanin dawainiyar karatun ‘ya’yansu.

 Markazi ya nuna godiyarsa ga Shaikh Dahiru Bauchi da addu’ar Allah ya saka masa da mafificiyar alkairi a bisa daukaka darajar ilmin addini da yake kan yi a fadin kasar nan. Babban baki a wajen taron, Dakta Fatihi Sheikh Dahiru Bauchi malami a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere, da kuma Dakta Adamu Usman Kobi shugaba tsangayar ilimin addini da ke jami’ar Jihar Bauchi ta Itas Gadau sun gabatar da jawabi kan muhimmancin ilimi da kuma cewar it ace hanya mafi sauyi ta ciyar da tattakin arzikin kasa da kawo karshen matsalar tattalin arziki. Sun bukaci gwamnati a kowace matakai da suke bayar da tasu gudunmawa da kuma zuba jari a sashin ilimi domin a samu gina al’umma ta kwarai a rayuwar gobe don tabbatar da Nijeriya ta kai munzalin da kowa ke fatan ta kai.



Source from: HAUSALOADED.COM

Post a Comment

 
Top