Kakakin majalisar dattijai kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Bukola Saraki ya bugi kirjin cewa babu wanda ya isa ya saukeshi daga mukaminshi na kakakin majalisar.


Saraki ya bayyana hakane a jiya, Lahadi a jihar Naija yayin da yake ganawa da manema labarai kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito, yace maganar tsigeshi daga kakakin majalisa da APC suke yi sun san ba abu bane me yiyuwa ba saboda basu da rinjayen da zasu yi hakan.

Haka kuma maganar cewa yayi murabus daga mukamin nashi abune wanda ba zai yiyu ba saboda shi yana kare muradin Najeriya ne ba ra'ayin kanshiba.

Ya kara da cewa, maganar tafiya hutu da sukayi tana kan tsari ba wai kawai sun yi ta ne dan son ransu ba, saida kowa a cikinsu ya amince sannan suka tafi kuma zasu dawo aikine idan ranar da suka amince da dawo aiki ta zo.

Post a Comment

 
Top