Wani matashi ya yi mai amfani da shafin sada zumunta na instagram, @captainblazee ya nuna wani bidiyo hotuna aka ce wani d'an siyasa a Legas ya sace azzakarin wani mai gadi bayan ya bashi kudi a City Hall.

A cewar @captainblazee, mai gadin ya nemi azzakarinsa ya rasa bayan ya karbi kudi daga hannun d'an siyasan kamar yadda muka samu daga shafin Linda Ikeji, Da ya ke wallafa bidiyon a shafinsa na instagram, ya yi takaicin yadda lamura ke tabarbarewa a Najeriya.

"Ina zamu je a Najeriya! Lokacin wani taron siyasa da aka yi a City Hall da ke Legas. Wani mai gadi ya yi ikirarin cewa azzakarinsa ya bace bayan wani mutum da ya zo a wata babban motan alfarma ya bashi kudi. Ya yi ta ihu yana neman taimako amma babu wanda ya iya tsayar da motar har da 'yan sanda," inji @captainblazee

Saura kadan mai gadin ya rasa rayuwansa a lokacin da wanda ake zargin ya ke kokarin guduwa a motarsa bayan 'yan sanda sun fara harbin motan akar she ya dawomasa da azzakarin nasa bayan kaduwa da ya yi ga uban gumi da ya jika kayansa sharkaf.

@wakiliya

Post a Comment

 
Top