Kungiyar wadda ta shirya kwararrun likitoci domin gudanar da wannan aikin, tace wannan taimakon ya shafi kowa da kowa ne musulmi da kuma wanda ba musulmi ba,
Wannan wani sabon tsari ne aka fito da shi, Wanda duk jihar da Za'a yi wa'azin kasa, zasu amfana da wannan shirin, kamar yadda mataimakin na musamman a ofishin shugaban Izala na kasa ( Ustaz Usman Funtua) ya bayyanawa manema Labarai a Wurin bikin sallamar marasa lafiyan .
An samu nassarar yiwa mutum 52 tiyata a ido, mutum 192 kuwa tabarau aka basu domin matsalar su bata Kai sai anyi musu aiki ba, a inda ragowar 256, suka samu nassarar samun magungunnan da zasuyi amfani da shi akan matsalar su.
"Da fatan zakuyi amfani da wannan gani Wurin ayukan Ibadah domin nuna godiya ga Allah akan mayar muku da ganin ku da yayi bayan har kun yanke kauna" inji shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala lau, Wanda shugaban kungiyar Izala na jihar kebbi, Ustaz Aliyu Abubakar jega ya wakilta a Wurin taron sallamar wadanda aka yiwa aiki anan Birnin
Post a Comment