Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool kuma dan asalin kasar Masar, wato Mohammed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na magoya baya wato FSF. Salah ya lashe kyautar ne Inda ya doke abokan takarar tasa wato Eden Hazard na Chelsea da Kun Aguero Sergio da Raheem Starling na Manchester City da Harry Maguire na Leceister da kuma Birgil Ban Dijk na Liberpool, inda ya lashe kyautar da kuri’u 366,000. Danwasan mai shekaru 26 ya lashe kyautar ne sakamakon ya taimakawa kungiyar tasa taje wasan karshe a gasar zakarun turai sannan kuma a yanzu haka a wannan kakar ya zura kwallaye guda 9. Salah ya ce
“nayi matukar godiya da wannan kyautar dana samu daga magoya baya domin kune kuka zabeni, sannan ko wacce kyauta na samu nakan sadaukar da ita ga abokan wasana na Liberpool amma yanzu wannan kyautar na sadaukar da ita dungurungun ga magoya bayan Liberpool”.
A shekarun baya ‘yan wasan Liberpool guda biyu sun taba lashe wannan gasa wato Suarez da Coutinho lokacin suna buga wasa a Liberpool, yanzu ma ga Mohammed Salah ya lashe. A kakar wasan data gabata dai Muhammad Salah ne ya lashe kyautar dan wasan dayafi kowannr dan wasa zura kwallo a raga a gasar firimiya bayan ya zura kwallaye 32 sannan kuma ya zura kwallaye 10 a gasar cin kofin zakarun turai.
Post a Comment