Suna: Cigaban Dadin Zama
Tsara Labari: Hamza Gambo Umar
Kamfani: 360 film production
Shiryawa: Nafi’u Gwammaja
Umarni: Sunusi Oscar 442
Jarumai: Nuhu Abdullahi, Garzali Miko, Hamza Gambo Umar, Maryam Ceetar, Zpeety, Hajiya Aisha Yola. Da sauran su. A farkon fim din an nuna Habiba (Z-Preety) tana sharar tsakar gida da tsohon ciki a jikin ta, a sannan ne mijinta Halilu (Garzali Miko) ya dawo daga gona, ganin tana shara ne ya nuna rashin jin dadin sa saboda tsohon cikin dake jikin ta, nan ya karbi tsintsiyar ya share mata gidan. Halilu ya cigaba da nunawa matar sa Habiba tsananin soyayya sam ba ya yarda tayi duk wasu ayyukan gida, wanki da debo ruwa duk shi yake yi mata don kada ta sha wahala, idan kuma tana bacci sauro ya dameta yakan tsaya a kan ta da mahuci yana yi mata fifita har zuwa lokacin sallar asuba. Kwatsam wata rana Halilu yaje gona sai aka dauko shi aka kawo shi gida baya motsi ba’a san ciwon da ya kama sa ba, nan fa aka dukufa wajen yi masa maganin gargajiya, ya zamana kullum Habiba ce take hidimar gidan gaba daya, itace take fita debo ruwa haka kuma ita take kwana wajen yi masa fifita cikin dare don gudun kada sauro ya damesa, duk da tsohon cikin dake jikin ta amma a haka take yin komai na gidan yayin da shi kuma Halilu sai sai kawai in yaga tana aiki ya kalle ta ya zubda hawaye saboda ko magana baya iya yi balle motsi da jikinsa. Yayin da a bangare daya kuma gidan su Amadu (Nuhu Abdullahi) ya hadu da jarababbiyar mata wato Lami (Maryam Ceetar) wadda ba ta son zaman lafiya, wadda ko kudin cefane ya bata sai ta raina kudin ta nuna ba zata yi girkin ba, idan mahaifiyar sa ta fito daga dakin ta ta nuna hakan ba daidai bane sai tayi fushi ta mikawa mahaifiyar sa kudin da nufin ita tayi girkin, idan Amadu ya yunkura zai yiwa matar sa Lami fada sai mahaifiyar sa ta hana shi gami da nuna cewar ya kyale Lami taci albarkacin juna biyun dake jikin ta. Haka Lami ta dinga tsuga rashin mutunci a gidan gami da fita unguwa ba tare da ta tambaya ba, sam ba ta ganin uwar mijin ta da daraja a kullum burin ta ta jawo abinda za’a yi fitina a cikin gidan, dalilin hakan ne yasa wata rana ta yiwa kanin mijin ta Audu (Hamza Gambo Umar) kazafin cewar ya leka ta a bandaki, ta rutsa shi a tsakar gida ta shake wuyan rigar sa da nufin ta hada shi rigima da yayan sa Amadu, amma saboda duk sun san halin ta sai aka gane cewar karya tayiwa Audu saboda ba’a san shi da halin da ta fada ba, ganin faruwar hakan ne yasa mahaifiyar su Amadi din wato (Hajiya Aisha Yola) ta umarci Audu akan ya kama gidan kakan sa da zama don a samu zaman lafiya. Ita kuwa Habiba haka ta cigaba da kula da mijinta mara lafiya wato Halilu, ya zamana cewa komai ita take yi masa, yayin da wata rana Amadu sun je gidan da nufin diba Halilu, ganin yadda matar Halilun take kula da shi ne yasa Amadu ya tuna da jarababbiyar matar sa wadda akwai lokacin da yake ciwon kai kamar zai mutu amma taki zuwa wajen mahaifiyar sa ta karbo masa magani, sai shi ya tashi ya fita da nufin zuwa wajen mahaifiyar sa amma da fitowar sa sai ya yanke jiki ya fadi ya suma, sai kanin sa Audu da mahaifiyar sa ne suka taimaka masa wajen yayyafa masa ruwa amma ita matar sa Lami da ta fito ba ta damu da halin da ya shiga ba. Haka Amadu ya gama tunani gami da jinjinawa matar Halilu har ya dauki kudi ya bata.
Kwatsam wata rana Habiba ta dawo daga gona wajen debo itace sai taga mijin ta Halilu ya samu lafiya ya warke, dalilin hakan ne yasa ta tsorata ta kira yayar mahaifiyar ta, anan ne Halilu ya fadi dalilin rashin lafiyar sa, nan duk akayi ta murna da warkewar sa, saidai kuma tun a ranar yana gama cin abinci ya rasu. Mutuwar Halilu ce ta daga hankalin matar sa Habiba har nakuda ta kama ta kuma ta haifi ‘yar ta mace. Yayin da ita kuma Lami a sannan ne mijinta Amadu ya sake bata kudin cefanen da bai gamsar da ita ba nan ta kawowa mahaifiyar sa ta bata sannan ta fada mata miyagun kalaman da suka janyo Amadu ya sake ta, ita ma bayan ta haifi dan ta namiji Amadu ya amshi dan sa ya cigaba da ba shi tarbiyya. Habiba kuwa sai da ta dau tsahon shekaru bakwai bata sake aure ba saboda tana ganin cewar ba zata sake samun namijin da zai kaunace ta kamar tsohon mijin ta Halilu ba. Yayin da shi kuma Amadu yaji a duniya babu wadda yake so da aure sai Habiba amma sam taki amincewa da bukatar sa saboda kudurin da ta bari a ran ta na rashin sake yin aure. Haka dai Amadu ya dage akan son auren ta yayin da mahaifiyar sa ma ta shige masa gaba suka cigaba da rarrashin Habiba sai da kyar ta amince ta aure shi don yiwa iyayen ta biyayya ba wai don tana son Amadu din ba saboda tana ganin ba zai so ta kamar tsohon mijinta da ya rasu ba. Bayan auren Habiba da Amadu sai ta ga ya na nuna ma ta tsananin kaunar da tafi wadda mijin ta Halilu ya nuna mata, domin har girki shi yake yi mata, baya son bacin ranta kuma yasan abinda take so sannan kuma baya bari tayi duk wasu ayyukan wahala. Bugu da kari kuma ya rike mata ‘yar ta Nana bisa gaskiya kamar yadda ya rike dan sa Abba wanda Lami ta haifa masa. Hakan ne yasa Habiba ta tabbatar da cewar tayi dacen miji domin akwai lokacin da kanin sa Audu ya kawo musu ziyara gidan sai take tabbatar masa da ta kasa gane wanda yafi son ta a tsakanin tsohon mijinta Halilu da kuma Amadu yayan sa. Daga karshe kuma sai ta tabbatar da cewar ashe don mijin mace ya rasu zata iya samun kamar sa ko wanda ya fisa da komai a rayuwa.
Abubuwan Birgewa:
1- Fim din ya fadakar kuma ya nishadantar, sannan kuma labarin ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba.
2- An samar da wuraren da suka dace da labarin.
3- Camera ta fita radau haka sauti ma ba laifi.
4- Wakar fim din ta nishadantar haka ma “sound track” din fim din yayi dadi.
5- Daraktan yayi kokari wajen ganin labarin ya tafi yadda ya dace, haka ma yayi kokari wajen ganin jaruman sun taka muhimmiyar rawa.
6- Soyayyar Habiba (Z-Preety) da Halilu (Garzali Miko) ta kayatar gami da taba zuciyar masu kallo. Kurakurai: 1- Yanayin yadda a farkon fim din aka yi ta yin sina-sinai (scenes) a tsakar gidan Halilu (Garzali Miko) kuma shi da matar sa kadai, hakan yaso yayi tsaho, ya dace idan an hasko gidan Halilu ko sau biyu ne sai a hasko kuma gidan su Amadu, amma ba’a yi hakan ba har sai bayan an yi sina-sinai kusan shida a jejjera a waje daya. 2- Bayan Halilu ya kamu da larurar da ba’a san dalilin afkuwar ta ba, me kallo yaga Habiba matar sa tana yin hidimar gidan gaba daya, amma ba’a ga an sauya masa kayan jikin sa da ya kwanta ciwo da su ba har zuwa sanda ya rasu, duk da an nuna ya dau tsahon lokaci yana jinya. Ya dace a sauya masa tufafin jikin sa ko sau daya ne, idan ma Habiba ba zata iya hakan ba to ya dace ko Amadu ne ya sauya masa tufafin tun da an nuna dan uwan ta ne wanda yake shiga gidan ya duba jikin mara kafiyar. 3- Ko sau daya ba a yi maganar za a gwada kai Halilu asibiti ba duk da larurar da ta same shi wadda ba ya iya morawa kansa komai. Shin kauyen babu asibiti ne? Tun da ba a nuna cewar talakawan kauye bane marasa hali ya dace a samar da dalilin rashin kai sa asibiti ko da ta hanyar cewa an kai shi asibitin amma bai warke ba. 4- An nuna mahaifiyar su Amadu (Nuhu Abdullahi) da kanin sa Audu (Hamza Gambo Umar) amma ko sau daya ba’a ga mahaifin su ba, shin ina mahaifin na su ya ke? Idan kuma mutuwa ya yi, to ya dace ko a baki ne a fadi hakan. Karkarewa: Fim din ya fadakar sosai, kuma an yi kokari wajen gina labarin ta sigar nishadantar wa gami da fito da kyakykyawan sako ga wasu matan wadanda idan mijin su nagari ya mutu ba sa sake yin aure saboda tunanin cewa ba zasu sake samun kamar sa ba, sai gashi an nuna cewar mace zata iya samun har wanda yafi mijinta nagarta idan ta mika lamarin ta ga Allah kuma ta sake yin aure.
©leadershipayau.com

Post a Comment