Daga Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar addinin Islama ta JIBWIS ta gana da manema labaru inda ta baiyana kammala shirin ta don kaddamar da aikin da zai kai ga kafa hukumar ba da lasisin halal ga kayan abinci da abin sha.
Taron dai da ya hada da hadin guiwar wasu kwararru zai gudana ne a birnin Lagos kudu maso yammacin Najeriya a watan Janairu mai zuwa 2019.
Shugaban JIBWIS ya ce shirin zai share hanya ga masu fataucin kayan abinci na Najeriya su samu lasisin shahararren kamfanin nan na HALAL don kai hajar su kasashen musulmi kamar Saudiyya, Sudan, Malaysia, Indonesia, Pakistan da sauran su.
“A lissafin irin wadannan kayayyaki na kasuwanci za a ci riba mai yawa sama da TIRILIYAN 2 na dala wanda ta hanyar kasuwar HALAL zaka samu” inji Sheikh Bala Lau. Shirin dai zai shafi dukkan kungiyoyin addinin Islama da sauran ‘yan kasuwa da hakan zai jawowa Najeriya samun dinbin kudin shiga.
Yanzu haka dai, kungiyar da kwararrun na tuntubar hukumomin da su ka dace don samun rejistar fara aikin wannan lasisi.
Post a Comment