Shirin na dauke da Sakkonni Uku- Inji Wanda ya Bada Umarni
A wani shirin hausa wanda aka fi sani da Fina-finan Kanywood da ake haskawa a Film House Sinima da ke Kano, shirin ya samu daukan hankalin masu kallo bisa yadda jama'a ke cocorindon zuwa kallo duba da irin sakonnin da ya ke dauke da su ga maza da mata musamman ma'aurata.
A zantawan wakilin Zuma Times bayan haska shirin a karo na biyu a Birnin Kano da babbar jarumar Shirin Wadda ta fito a matsayin Dr. Haleema, Maryam Isah Abubakar ta bayyana cewa shirin babban sako ne ga ma'aura bisa irin lamura da ke cika faruwa a tsakanin a gida.
“Fim din ya nuna illar rashin yabon mata daga mazajensu. Mu mata akwai mu da son a yabamu domin mu yi fiye da haka ko da abin bai kai matsayin a yaba mana ba.Inji Maryam Isah.
Shima a nashi bangaren, babban wanda ya ba da umarnin shirin Abubakar AS Mai Kwai ya bayyana cewa, shirin babbar shiri ne wanda za a dauki fiye makonni Biyu ana haskawa.
Ya ce shirin na dauke da sakonni Uku wanda suka hada da Illar yin Social Media ga mace mai aure, rashin yabon mace daga mijinta da kuma irin mu'amala da mace mai aure ta ke yi a gurin aiki da maza.
“dukkan sakonnin da wannan Fim din ke dauke da su na yawan faruwa a tsakanin yawancin ma'aurata wanda dalilin haka ne ya sa muka shirya wannan Fim domin nuna al'uma illar hakan". A cewar Darakta Mai Kwai.
Draktan ya ce akwai matukar illa ga mace me aure da ta ke yin Social Media wanda mafi muni ma ta rika sanya hotunanta. “Haka ma ga mace mai aure da ta rika sanin yadda za ta rika suturce jikinta a yayin fita gujin aiki da zai sa ta yi mu'amala da maza".
Ya kuma kara da bayyana mata na bukatar yabo daga mazajensu musamman idan suka yi abin burgewa, domin hakan na kara musu karfin gwiwar yin fiye da haka.
Daga karshe mai bada Umarnin tare da jarumar shirin sun yi godiya ga wadan da suka samu damar zuwa suka kalla tare da kira ga wadan da basu kalla ba da su hanzarta zuwa su kalla ko su saya domin kallo idan Fim din Dr. Halima ya fito a kasuwa.
Shirin ya samu jarumai da suka hada da Ali Nuhu, Maryam Isah Abubakar, Aminu Shariff, Hafsat Idriss, Babbale Hayatu da dai sauransu.
©Zuma Times Hausa.

Post a Comment