Wasu gungun yan bindiga da suka yi garkuwa da wata mata mai suna Sumayya Abubakar dake dauke da juna biyu a tare da ita, a kwanakin baya sun sanar da yan uwanta cewa zasu kasheta idan har ba’a biyasu kudi naira miliyan ashirin cikin sa’o’I 24 ba.
Jaridar Premium Times ta ruwaito haka bayan tattaunawa da tayi da mahaifnta, Malam Abubakar Yusuf, wanda yace a yanzu haka yan bindigan sun kashe wani yaro makwabcinsu da suka yi garkuwa dashi tare da Sumayya, Surajo Umar domin su nuna abinda zasu iya.
Majiyar Legit.com ta ruwaito tun a watan Oktoba ne aka yi garkuwa da Sumayya da Umar da wasu mutane guda hudu a kauyen Dauran dake cikin karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara.
A hirar da mahaifin sumayya yayi da majiyarmu, ya bayyana cewa iyalansa da danginsa gaba daya sun shiga mawuyacin hali tun bayan sace Sumayya, inda ya tabbatar da tana dauke da juna a biyu a lokacin da suka yi garkuwa da ita.
“Halin da diyarmu take ciki na rashin ci da sha a kungurmin daji hali ne mai tsanani, balle kuma tana dauke da juna biyu, yan bindigan sun nemi mu biyasu naira miiyan 150, daga bisani suka rage zuwa naira miliyan 30, miliyan 20 na Sumayya, miliyan 10 na Surajo.
“Kaga, a ranar da aka sako tagwayen matannan, iyalan gidana sun shiga cikin alhini wanda har ta kai ga bama iya cin abinci, saboda a duk lokacin da tuna halin diyata ke ciki, sai naji tamkar zuciyata zata fashe.” Inji shi.
A cewar mahaifin Sumayya, zuwa yan sun tara kudi naira miliyan biyar da taimakon wani dan uwansu, Lawalli Dauda, wanda ya kai ma yan bindigan kudin da kansa, amma suka kamashi a zatonsu mahaifin Sumayya ne.
A yanzu haka dai yan bindigan sun tabbatar ma mahaifin Sumayya cewa sun kashe dan makwabcinsa Surajo, kuma ba zasu saki Sumayya da Lawwali Dauda ba har sai an biyasu naira miliyan ashirin cikin sa’o’I 48 daga ranar Talata, a yanzu sauran awanni 24, idan bah aka ba zasu kashesu.
Post a Comment